Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kwarmata Bayanan Ganawar Trump Da James Comey


An kwarmata bayanan da babban daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka James Comey ya rubuta, bayan ganawa da dama da yayi da shugaban Amurka Donald trump a shekarar da ta gabata, jiya Alhamis.

Comey ya ce ya rubuta bayanan ne jim kadan bayan da suka yi magana da shugaban na Amurka, saboda bai amince da ganawar tasa da shugaban ba.
A cikin bayanan Comey ya rubuta cewa, shugaban ya damu da ikirarin da ake yi na cewa ya hada kai da Rasha domin taimakawa wajen cin zaben shugaban kasa da kuma batun wani faifan bidiyo na Trump da wasu mata masu zaman kansu 'yan kasar Rasha.
A wani bayanin da ya rubuta bayan tattaunawa da Trump a ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2017, Comey ya rubuta cewar Trump yace yana kokarin gudanar da mulkin shi amma wannan kazafin na Rasha na neman kawo mishi cikas.
Bangaren shari'a na Majalisa ne dai suka fitar da wannan takardun nuni wanda daga baya manema labarai suka samu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG