Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump na adawa da gina karamin kamfanin Ford a kasar Mexico


Donald Trump na jam'iyyar Republican mai neman jam'iyyar ta tsayar dashi takarar shugaban kasa
Donald Trump na jam'iyyar Republican mai neman jam'iyyar ta tsayar dashi takarar shugaban kasa

Siyasar kasuwanci ta ja hankali a wannan makon, biyo bayan sanarwa da kamfanin kira motoci na FORD ya bada, na cewa zai bude karamar cibiyar kera motocinsa a birnin San Lius Potosi da ke kasar Mexico, wanda zai dauki ma’aikata akalla Dubu 28 nan da zuwa shekarar 2020.

Dan takarar shugabancin Amurka na sahun gaba a Jam’iyya Republican Donald Trump yayi Allah wadai da wannan magana ta kamfanin, inda yace wannan abin kunya ne, kasancewar kamfanin zai kwashe damar samun aikin Amurkawa ya kai wata kasa ta daban.

Wannan dai ba sabon al’amari bane ga Trump, da dama ya fada tun a farkon bayyana maganar takararsa a watan Yunin bara, lokacin da yace, zai janye maganar cewa Ford bas a biyan ko kwabo wajen shigo da kayansu zuwa Amurka. Damar da suka samu daga yarjejeniyar kasuwancin Amurka ta Arewa.

Trump yace, duk wata mota ko na’urar da aka kera kamfanin da ke waje, to tabbas sai sun biya akalla harajin kaso 35 daga cikin 100 don shigowa da kayan zuwa nan cikin Amurka. Dan takarar Democrat Bernie Sanders ya sha kushe abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton game da wannan doka ta rashin biyan harajin shigo da kaya, duk da yake dai ita ta nuna kin abin daga baya wanda a da ta amincewa lokacin tana Sakatariyar wajen Amurka.

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG