Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Duba Yiwuwar Rufe New York, New Jersey


Yayin da Trump yake magana da manema labarai a ranar 28 ga watan Maris, 2020, a Washington
Yayin da Trump yake magana da manema labarai a ranar 28 ga watan Maris, 2020, a Washington

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar rufe jihohin New York, New Jersey da kuma Connecticut a wani mataki na dakile yaduwar cutar coronavirus a kasar.

Trump ya ce za a rufe jihohin ne na dan wani lokaci domin kada cutar ta kara samun matsuguni a jihohin da mutane ba su kamu da yawa ba.

Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a ranar Asabar.

Ya kara da cewa, ya yi magana da wasu gwamnonin kasar ciki har da na jihar Florida Ron DeSantis, wadanda suka nuna mai cewa akwai bukatar a dauki wannan mataki.

Sai dai gwamnan jihar New York, Andrew Cuomo wanda dan jam’iyyar Democrat ne, ya soki wannan yunkuri na Trump yana mai cewa ba su tabo wannan batu ba yayin da Suka yi wata ganawa da shugaban a ranar Asabar.

“Ni ban ma san abin da yake nufi ba, ban kuma san yadda za a aiwatar da wannan mataki ba kuma idan ka kalle shi ta fuskar kiwon lafiya, ban san me ake so a cimma ba.” In ji gwamna Cuomo

Doka dai ta ba gwamnatin tarayyar Amurka karfin ikon da za ta hana yaduwar cututtuka a tsakanin jihohin kasar, amma hakan bai fayyace ko shugaba Trump zai iya ba al’umomin jihohin umurnin su zauna a gida ba.

Kalaman na Trump na zuwa ne bayan da ya ba da umurni wani jirgin ruwan sojin kasar mai dauke da asibiti a cikinsa ya kai wa jihar ta New York dauki a fannin kula da marasa lafiya.

New York ita ce jihar da ta fi kowacce yawan wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 inda take da mutum 26,700 cikin mutum sama da 100,000 da cutar ta harba a duk fadin kasar a cewar wata kididdiga da Jami’ar John Hopkins ta yi.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG