Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Nazarin Yadda Za a Warware Matsalolin Wariya


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Ana sa ran cewa, shugaban Amurka Donald Trump zai gana da shugabannin addinai, jami’an tsaro da masu kananan sana’o’i a yau Alhamis a birnin Dallas, yayin da yake duba yiwuwar daukar matakai akan zanga-zangar da ake yi a fadin Kasar biyo bayan mutuwar ba-Amurken nan bakar fata, George Floyd.

Bayanai daga fadar White House sun nuna cewa, za a duba yadda za a warware matsalalolin wariya a batutuwan da suka shafi tarihin tattalin arziki, lafiya da shari’a tsakani al’ummomin a Amurka.

Mai Magana da yawun fadar white house Kayleigh Mcenany, ta sanar da manema labarai a jiya Laraba cewa, gabadaya, da mahukunta da bangaren shugaban kasa suna duba yiwuwar daukar matakai da nan bada jimawa ba zasu aiwatar.

Bukata daya da Trump baya goyon bayanta itace, canza dokar da take taimaka wa baiwa jami’an tsaro kariya daga fuskantar tuhumar cin zarafin jama’a a kotu.

Shugabannin majalisar wakilai mai rinjayen ‘yan Democrats na gyaran fuska akan ka’idojin aikin ‘yan sanda wanda zai kara bada damar zartas da hukunci akan ‘yan sanda, a kafa wata regista da za a iya bibiyar halin ‘yan sandan da suka aikata ba daidai ba domin kawo karshen cin zarafi a fadin kasar.

Majalisar dattijai mai rinjayen 'yan Republicans, suma suna aiki akan wata gyara kana, ana sa ran kwamitin shari’ar majalisar zai yi zama akai a makon gobe.

Kwamitin shari’ar majalisar wakilai a jiya yayi zama, inda dan'uwan Floyd, Philonise ya bukaci 'yan majalisar suyi dokar da zata haramta wa ‘yan sanda yin amfani da karfin tsiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG