Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Bada Umurnin Gina Katanga Kan Iyakar Kasarsa da Mexico


Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Donald Trump, jiya Laraba ya bayar da umurnin a gina katanga a kan iyakar kasar da Mexico don shawo kan kwararowar bakin haure, yayin da ya kuma yi barazanar janye kudaden da ake baiwa wasu daruruwan biranen Amurka masu bayar da mafaka ga bakin hauren.

Trump ya yi amfani da ikonsa na Shugaban kasa wajen rattaba hannu kan batun bakin haure, yayin da ya ziyarci Sashin Tabbatar Da Tsaron Gida, wanda shi ne sashin da aka baiwa aikin kula da kan iyakokin Amurka.

"Mu na cikin wani yanayi na rudami game da kan iyakarmu ta kudu. Kwararowar bakin haure daga kasashen yankin tsakiyar Nahiyar Amurka na illa ga Amurka da Mexico," a cewarsa. Ya kara da cewa, "Kuma na yi imanin cewa matakan da za mu dauka, wadanda za mu fara daga nan wurin, za su inganta lafiyar jama'a a kasashen biyu. Hakan zai amfani Mexico gaya."

Wannan umurnin Shugaban kasan, wani ruri ne game haramar cika alkawarin da ya yi yayin yakin neman zabe -- inda ya yi ta cewa bakin haure na barazana ga tsaron Amurka, sannan su na raba Amurkawa da ayyukan yi. A wurare daban-daban na yakin neman zabensa, magoya bayansa na kud-da-kud kan ce, "A gina katangar; a gina katangar!"

Trump ya gaya ma kafar labarai ta ABC cewa cikin watanni masu zuwa za a fara aikin gina katangar, sannan ya cigaba da cewa Mexico za ta biya kudin gina katangar.

Trump ya ce hanyoyin da Mexico za ta biya na iya kasancewa da wuyar fahimta ga wasu, wanda ke nuna alamar cewa ba wai kasar ta Mexico za ta mika ma Amurka kudi ne kai tsaye ba.

XS
SM
MD
LG