Duk da cewa yawancin Amurkawa shugaban Amurka Donald Trump suke dorawa laifin tsawaita rufe ma’iakatun gwamnatin tarayyar kasar, shugaban na Amurka ya fadawa wasu manoma cewa ‘yan jam’iyyar adawa ta Democrats su ma suna da laifi wajen janyo rufe ma’aikatun.
Da yake jawabi a yayin wani babban taron manoma na kasa wanda aka yi a jihar New Orleans, Trump ya ce, ‘yan Democrats “ba za su yarda su ba mu abin da muke bukata ba domin tsare Amurkawa” ba.
Shugaban ya kare bukatarsa ta neman biliyoyin daloli domin gina katanga akan iyakar Mexico da Amurka, inda ya ce jirage masu tuka kansu da na'urori masu aiki da motsi, ba su isa a matsayin matakan tsaro ga iyakokin ba.
Trump ya jadadda cewa, ba zai taba janyewa ba daga kokarin da yake yi na kare Amurkawa.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 08, 2023
Ana Bikin Ranar Mata A Duniya
-
Maris 01, 2023
Shirin Sojojin Amurka Na Yin Nasara A Yaki Da Kasar China
Facebook Forum