Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Ya Yi Farin Cikin Sake Bullar Kim Jong Un Lafiya


Wata ganawar Trump da Kim

Shugaban Amurka Donald Trump, jiya Asabar, ya ce ya na mai farin cikin sake bayyanar Kim Jong Un da cewa Shugaban na Koriya Ta Arewa na cikin koshin lafiya.

“Ni dai kam, Ina farin cikin ganin ya dawo, kuma lafiyarsa lau!” sakon da Trump ya tura kenan ta kafar twitter, bayan bullowar Kim cikin jama’a a karon farko cikin makwannin kusa uku bayan an yi ta yada jita jita sosai cewa ya na fama da tsananin rashin lafiya ko ma watakila yam utu.

Gidan talabijin din gwamnatin Koriya Ta Arewa ya nuna Kim yana tafiya, ya na murmushi sosai kuma yana zugar tabarshi a wani wurin da Koriya Ta Arewar ta ce wani kamfanin takin zamani ne da ake bukin budewa ranar Jumma’a a Sunchon, arewa da Pyongyang, babban birnin kasar.

Jita jita game da makomar lafiyar Kim ta yawaita tun bayan da aka kasa ganinsa ranar 15 ga watan Afrilu wurin bukin ranar haihuwar kakansa, wanda ya assasa kasar ta Koriya Ta Arewa – wadda it ace ranar da ta fi kowacce muhimmanci a kasar a siyasance.

Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG