Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Jaddada Aniyarsa Ta Hana Jariran Baki Zama Amurkawa


Shugaba Donald Trump yana so ya yi wa kundin tsarin mulkin Amurka gyara don kawar da dokokin da suka bai wa yaran baki da aka haifa a nan Amurka damar zama yan kasa.

A gangamin taron siyasa da ya yi jiya Alhamis a garin Columbia da ke Jihar Missouri, Shugaba Donald Trump ya sake bayyana aniyarsa ta yi wa kudin tsarin mulki Amurka gyara don kawar da dokokin da suka bai wa duk wanda aka haifa a nan Amurka damar zama dan kasa.

Shugaban ya fada a wajan gangamin cewa shi baya goyon bayan 'yan fakewa su zo su haihu, inda mata da suke da ciki daga wasu kasashe suke tahowa nan Amurka su haihu don jariransu su zama 'yan kasar na Amurka.

Dangane da hakan ne Trump ya ce yana so ya yi wasu sauye-sauye ga babi na 14 na kundin tsarin mulki Amurka.

Amma masu sharhi akan harkarkokin shari’a sun yi watsi da ikirarin navsa da ya yi, inda suka ce ya fi karfin ikon shugaban kasa ya canja kundin tsarin mulkin Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG