Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kalubalanci 'Yan Majalisa Kan Tsaurara Matakan Mallakar Bindiga


Shugaban Amurka, Donald Trump, yayin da yake ganawa da 'yan majalisun dokokin Amurka kan yadda za a samar da tsaro a makarantu
Shugaban Amurka, Donald Trump, yayin da yake ganawa da 'yan majalisun dokokin Amurka kan yadda za a samar da tsaro a makarantu

A yau Alhamis, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya jaddada bukatar a samar da tsauraran matakan mallakar bindiga a kasar domin a magance matsalar harbe-harbe a makarantu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin kira ga ‘yan majalisar dokokin Amurka da su amince da wasu matakai da za su takaita saurin mallakar bindiga, domin a kaucewa harbe-harben da ake yi a makarantu.

Wannan kira na zuwa ne makwanni biyu, bayan da wani dan bindiga ya harbe mutane 17 a wata makaranta da ke jihar Florida.

Shugaba Trump ya sake waiwayan wannan batu ne a yau Alhamis a wani sako da ya aike ta shafinsa na Twitter, kwana guda bayan da ya karbi bakuncin ‘yan majalisar dokokin, inda suka tattauna kan wannan batu.

Yayin wannan ganawa, shugaba Trump, ya zargi ‘yan majalisar da “nuna tsoron” kungiyar wadanda suka mallaki bindiga, wacce ke kare muradun mambobinta.

Shugaban ya kara da cewa, “zai yi zurfin tunani” kan yadda za a kara yawan shekarun da ya kamata mutum ya kai kafin a sayar mai da bindiga, kamar bindigar AR- 15, wacce aka kai harin na Florida da ita.

Trump yana so ne a kara shekarun mallakar bindiga daga 18 zuwa 21.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG