Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kara Zafafa Cecekuce Akan Korar Shugaban Hukumar FBI


Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Donald Trump na Amurka ya kara zafafa cece-kuccen dake tsakaninsa da mutumin da ya kora daga mukamin shugabancin hukumar binciken manyan laifukka ta Amurka ta FBI, James Comey.

Trump ya nuna alamar cewa akwai wasu faya-fayen asiri na magangannunsu da aka dauka ba tareda sanin shi Comey din ba, lokacinda suka gana a farkon wannan shekara.

A cikin wani sakon Twitter da ya aika da sanyin safiyar yau, Trump yace “ya kamata James Comey yayi fatar cewa Allah sa ba fayafayen magangannun da muka yi ba ne kafin yaje yace zaiyi wasu tone-tonen silili a kafafen yada labarai!”

A ranar Talatar da ta gabata ne Trump ya tsige Comey daga shugabancin hukumar ta FBI, a daidai lokacinda hukumar ke gudanarda bincike akan shisshigin Rasha a zaben Amurka na shekarar 2015 da zimmar neman ko akwai wata alaka tsakanin Rasha din da ‘yan Kweamitin din kyampen na shi Trump.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG