Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kasa Tabuka Abin Kirki Wajen Magance Bazuwar Coronavirus - Biden


Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden
Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, wanda ake ganin shi ne 'yan Demokrat zasu tsayar dan takarar shugaban kasa a zaben da za a gudanar a watan Nuwanba, ya zargi Shugaba Donald Trump, da jan kafa wajen dakile barazanar da cutar Coronavirus ta haddasa a kasar.

A cewar Joe Biden "Trump ya kasa tabuka komai wajen magance bazuwar annobar."

"Al'amari ne na gaggawa, kuma bana zaton ana yin hakan” a cewar Biden a wani shirin gidan talabijin na ABC mai suna This Week.

Ya fadi cewa Trump na bukatar yayi hanzari, ya gaggauta wajen magance bazuwar annobar.

Yayin da yake sukar Biden a baya bayan nan, a jawabinsa ga manema labarai, Trump ya yaba da yabonsa da yayi game da matsayin da ya dauka na dakatar da saukar jirage daga China, a lokacin da aka bada sanarwar barkewar cutar Coronavirus a birnin Wuhan na kasar China.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG