A wani abu da ake ganin mataki ne na hukunta wadanda suka ba da shaida a gaban Majalisar Dokokin Amurka, yayin zaman jin bahasin shirin tsige Shugaba Donald Trump, gwamnatina ta kori wasu jami’anta biyu.
Wadannan jami'ai su suka ba da "mummunar" shaida a lokacin binciken da majalisar wakilai ta yi, har ta kai ga tsige Trump.
Da farko rahotanni sun nuna cewa, Shugaba Trump ya kori Laftar Kanar Alexander Vindman, babban jami’in tsaro a Fadar White House, wanda ya taka muhimmiyar rawa a shirin tsige shugaba Trump da ‘yan Democrat suka yi yunkurin yi.
Lauyan Vindman ya ce, a jiya Juma’a aka umurci Vindman da ya fice daga Fadar ta gwamnatin, saboda abin da aka ayyana a matsayin “ramuwar gayyar fadin gaskiya da ya yi.”
Sannan har ila yau, an sallami dan uwan Vindman Laftar Kanar Yevgen Vidnman daga Fadar ta White House, kamar yadda wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar ta nuna.
Jami'an biyu 'yan tagwaye ne.
Bayanai sun kuma yi nuni da cewa, an mayar da wasu wani sashi cikin rundunar sojin Amurka.
Baya kuma ga haka, akwai rahotanni da ke nuna cewa, an kuma sallami Gordon Sondland, jakadan Amurka a kungiyar Tarrayyar Turai.
A tsakiyar makon nan, Majalisar Dattawa mai rinjayen 'yan republican, ta wanke Trump daga tuhume-tuhumen da suka kai ga tsige shi a majalisar wakilai mai rinjayen 'yan Democrat.