Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump ya Kyautata Zaton Tattaunawa tsakanin Korea ta Arewa da ta Kudu Zai Zarce Batun Wasanni


Shugaba Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana tattaunawar ba-saban ba da za a yi yau Talata tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa a matsayin “Babban yunkuri,” yana fatan tattaunawar zata zarce batun maganar shigar Koriya ta Arewa wasannin Olympic na wata mai zuwa, ta kai ga taba sauran muhimman batutuwa.

A yau Talata ne wakilai daga kasashen biyu, wadanda a hukumance har yanzu suna cikin halin yaki da juna, zasu gana a kauyen Panmunjob, wanda ake kira kauyen zaman lafiya dake kan iyakar kasashen biyu, kuma inda aka rattaba hannu a yarjejeniyar sulhu ta shekarar 1953 wadda ta kawo karshen fada a tsakanin kasashen biyu.

A jawabinsa na sabuwar shekara, shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ya ce zai aika da ‘yan wasan kasarsa zuwa gasar wasannin Olympics zuwa Koriya ta Kudu, jim kadan bayan da yayi barazanar cewa yana da madannin makaman nukiliya akan teburin ofishinsa, da zai iya harbawa zuwa Amurka.

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in, wanda ke neman sasantawa da Koriya ta Arewa, ya mayar da martani ta hanyar mika goron gayyatar tattaunawa ga gwamnatin Kim.

Tattaunawar da za a yi yau Talata, ana kyautata tsammanin zata mayar da hankaline kan gasar Olympics, da kuma ko ‘yan wasan Koriyoyin biyu zasu yi tattaki tareda juna a lokacin shagulgullan bude gasar.

Za kuma a iya shigar da wasu batutuwa ciki kamar dawo da shirin hada iyalan kasashen biyu da kuma yadda za a inganta dangantakar kasashen biyu.

Babu hannun Amurka a cikin tattaunawar da za ayi ta yau Talata.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG