Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Sanya Hannu A Wata Doka Da Ta Shafi 'Yan Sandan Amurka


A daidai lokacin da ke ake gudanar da zanga-zangar kan titi a fadin kasar, ranar Talata 16 ga watan Yuni Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu a wata dokar shugaban kasa wadda ta zayyana garambawul din da aka yi wa ‘yan sandan kasar.

Dokar za ta karfafa "hukumomin 'yan sanda a fadin kasar su yi aiki da ka'idoji na kwarewa don yi wa al’ummominsu aiki. Wadannan ka'idojin za su kasance masu karfin gaske a doron duniya, a cewar shugaban.

Haka kuma, dokar ta bukaci cibiyoyin da ke bincike da bada horo kan cancanta su horar da jami’an kan dabarun kawar da yanayin da zai kawo tashin hankali da kuma ka’idodin yin amfani da karfi.

Wani bangaren dokar kuma ya bukaci a ƙirƙiro tsarin da ‘yan sanda za su yi aiki da jami’an kula da harkokin zamantakewa wajen amsa wani kira da suka samu wanda bai da nasaba da tada hankali, ta hanyar ware kudade daga gwamnatin tarayya don tallafa wa jami'ai wajen tunkarar mutanen da ba su da muhalli, da waɗanda ke da matsalar tabin hankali da kuma masu larurar shan miyagun kwayoyi a cewar Trump.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG