A yau Litinin, Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewar Washingto ta amince ta dakatar da shirinta na kakaba tsauraran haraji akan makwabciyarta dake kudu, kasar Mexico, tsawon wata guda, biyo bayan tattaunawa da shugabar kasar claudia sheinbaum.
Ya ce an yi tattaunawar cikin raha, inda ya kara a sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta cewa “mun sake amincewa nan take mu dakatar da karin harajin da ake tsammani tsawon wata guda wanda a wannan dan tsakanin za mu ci gaba da tuntubar juna.”
Tunda fari Shugaba Claudia Sheinbaum ta sanar da amincewa da dakatar da fara kakaba haraji akan kayayyakin Mexico tsawon wata guda, bayan tattaunawa da Donald Trump.
A matsayin wani bangare na jerin yarjeniyoyi, Mexico za ta tura dakarun tsaron kasa 10, 000 zuwa kan iyakarta da Amurka domin yaki da fataucin miyagun kwayoyi, kamar yadda ta sanar.
Dandalin Mu Tattauna