Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yabawa Mayakan Amurka


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

A matsayinsa na shugaban Amurka na farko da ke kan mulki da ya halarci faretin tunawa da tsofaffin sojoji a New York, da ajiye furanni a gandun Eternal Light Memorial, Donald Trump ya jinjinawa mayakan da suka halarci taron da dukan wadanda suka yi yaki a Amurka har lokacin yakin duniya na biyu.

“Za mu cigaba da karrama tsoffin sojojinmu,” Trump ya bayyana hakan ne jiya Litinin da safe a wajen bude bikin fareti karo na 100 da ake yi duk shekara.

Trump ya kuma bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, wanda binciken yuwuwar tsige shi ya cigaba da mamayewa a majalisar wakilai mai rinjayen ‘yan jam’iyyar Demokrat.

A lokacin da yake bada misalin samamen da dakarun Amurka na musamman suka kai a watan da ya gabata akan shugaban kungiyar IS, Trump ya ce, “al-Baghdadi ya mutu. Sannan mataimakinsa na biyu shima ya mutu kuma mun saka ido akan na uku mafi girma. Karshen ta'addancinsa ya zo, kuma makiyanmu suna gudu cikin yanayin tsoro sosai.

A ranar 31 ga watan Oktoban data gabata ne dai kungiyar ‘yan ta’addan ta tabbatar da mutuwar dadadden shugabanta, Abubakar al-Baghdadi, kuma ta bayyana wanda ya maye gurbinsa mai suna Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG