Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yabi Kungiyar Tsaro Ta Nato


Yayin da a baya shugaba Trump ya ke yawan cewa ana kwarar Amurka a kungiyar Tsaro ta Nato, yanzu kuma ya shiga yabon kungiyar saboda sun amince za su kara irin gudunmuwar da su ke bayarwa.

Yayin da kungiyar tsaro ta NATO ke shirin gudanar da babban taronta a nan Washington, inda za a yi bikin cikar kungiyar shekaru 70 da kafawu, Shugaban Amurka Donald Trump, ya fara yabon gamayyar kasashen da kuma shugabanta, a lokacin wani zama da suka yi da Sakatare Janar din kungiyar.

A cewar Shugaba Trump, an samu gagarumin ci gaba, ta fuskar raba daukan dawainiyar kungiyar a tsakanin mambobinta 29 masu cin gashin kansu.

Sai dai shugaban na Amurka, wanda ya yi wannan bayani yayin da yake karbar bakuncin Sakatare Janar na kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg, ya soki kasar Jamus, inda ya ce, ba ta ba da kason da ya kamace ta ba.

A nasa bangaren, Stoltenberg, wanda Trump ya yaba, ya nuna godiya ga shugaban na Amurka, kan yadda ya jajirce wajen ganin an raba daukan dawainiyar kungiyar.

Sai dai mai sharhi kan huldar kasa da kasa na majalisar Atlantic Council da ke nan Amurka, Mark Simakovsky ya ce, irin kalaman da shugaba Trump ya yi a baya, ya ragewa kungiyar ta NATO kwarjini a idon abokanan hamayyarta.

A bayan, shugaba Trump ya taba nuna rashin muhimmancin kungiyar tsaron ta NATO, inda ya kwatanta ta a matsayin wacce yayinta ya wuce.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG