Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yabi Kwamitin Binciken Katsalandan Din Rasha


Donald Trump

Yayin da, a daya gefen, Shugaban Amurka Donald Trump ya yabi kwamitin binciken da ya ce ya wanke shi, a daya gefen kuma, ya caccaki 'yan jam'iyyar Dimokarat, wadanda ya ce su na masu bita da kullin siyasa.

Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ke cike da farin ciki, ya yabi kwamitin bincike na musamman da Robert Mueller ya jagoranta, yayin da kuma yake kumfar baki kan bukatar da ‘yan jam’iyyar Democrat suka mika, ta a fitar da cikakken rahoton da ya binciki shisshigin da Rasha ta yi a zaben 2016, binciken da ya wanke Trump daga zargin cewa ya hada kai da hukumomin Moscow, amma ba tare da ya wanke shi daga zargin da ake yi cewa, ya yi kokarin hana binciken ba.


Yayin da yake magana a fadar gwamnatin White House, shugaba Trump, ya bayyana Mueller a matsayin mutum mai dattaku, yana mai cewa ya gamsu dari-bisa-dari- da rahoton binciken. Ya ce, “babu wani hada kai da muka yi da Rasha, babu kuma wani yunkuri na hana doka ta yi aikinta, wannan rahoto, ya tsame ni daga dukkanin wadannan zarge-zarge.”


Sai dai yayin da ya fitar da takaitacce bayani kan rahoton binciken na Mueller a ranar Lahadi, wanda ya karba daga hannun Muellern, Babban Atoni Janar din Amurka, William Barr, ya ce rahoton bai fidda matsaya ba, kan ko shugaba Trump ya aikata laifi, ko kuma ya yi yunkurin hana doka ta yi aikinta.
Shi dai Trump ya sha sukan kwamitin binciken na Mueller, inda ya rika kwatanta shi a matsayin “bita-da-kullin-siyasa.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG