Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yi Amfani Da Karfin Ikonsa Don Tabbatar Da Aiki a Gida


Trump
Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da ikonsa na Shugaban kasa, wajen rattaba hannu kan wani umurni, wanda zai sa ya zama da wuya kamfanoni su dau ma'aikatan wuccin gadi daga kasashen waje.

Umurnin, wanda ake kira, "Umurnin Sayen Na Amurka, Daukar Dan Amurka Aiki," zai fara aiki ne bayan wani tanajin da ke tafe da shi ya kwaskware tsarin takardar visa ta H 1-B.

Takardar visar ta H1-Bs ta amince ma kamfanoni - musamman ma na fasahar lataroni - su dau kwararru daga kasashen wace su yi aiki a AMurka na tsawon shekaru uku. Kowace shekara akan ware gurabe 85,000 na daukar irin wadannan ma'aikatan, inda gurabe 65,000 na masu digirin farko ne a yayin kuma 20,000 na masu digiri na biyu ko fiye.

"Za mu yi amfani da abin da dukkanninku ku ka sani sosai. Ana kiransa gudumu," a cewar Trump a yayin wani jawabi a kamfanin Snap-on Tools da ke Kenosha, Wisconsin a jiya Talata.

Gwamnati za ta dau matakin ganin cewa kamfanin na nuna shaidar cewa irin wadannan visa ana bai wa ma'aikatan da su ka yi matukar kwarewa ne a bangarensu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG