Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci gaba Da Kai Hare-hare Akan ‘Yan adawan Burundi -MDD


Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza

Kwamishinan dake kula da ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana kara samun damuwa kan yadda mayakan sa-kai da gwamnati ke mara wa baya suke kai hare-hare akan wadanda ke adawa da jam’iyar shugaba Pierre Nkurunziza a Burundi.

Ofishin kula da hakkokin bil adaman, ya ce ana samun munana hotunan bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta kan yadda ake cin zarafin bil adama.

“Wadannan matasan dake yekuwar yin fyade a Imbonekure a Lardunan Burundi, babban abin damuwa ne, domin kiraye-kirayen na su na kara tabbatar mana da irin labaran da wadanda suka tsere daga Burundin suke fada mana.” In ji Rupert Colville, wanda ya yi magana da yawun kwamishina Zeid Ra-ad Al Hussein.

A lokacin da hoton bidiyon ya fito baina jama’a a karon farko, jam’iyar CNDD-FDD mai mulki ta ce bidiyon na jabu ne kuma ba a cikin kasar ta Burundi aka dauka ba.

Amma bayan da ta amince cewa bidiyon na gaske ne, jam’iyar ta ce matasa sun rairai wata waka a wani gangamin jam’iyar wacce ba ta kunshe da irin manufofin jam'iyar.

Amma Colville ya ce, a mafi yawan lokuta akan samu shugabannin jam’iyar a irin wadannan taruka inda ake raira wannan waka, wanda hakan ke nuna goyon bayansu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG