Shugaba Trump ya gabatar da jawabin ne a gaban gamayyar Majalisun Dokokin kasar ta 116. Inda ya zargi wasu ‘yan siyasar kasar da baiwa bakin haure da suka shigo Amurka ta barauniyar hanya kariya.
Cikin jawabin Trump ya yi kira ga Majalisun kasar da su samar da dokar da za ta baiwa mutanen da bakin hauren suka yiwa laifi su yi ‘karan gwamnatocin.
Haka kuma Trump ya ce gwamnatinsa ta kare martabar addinai a Amurka, ciki har da abin da ya kira damar bari a yi adu’o’i a makarantu.
Ya kuma sha alwashin kare tsarin mulki da ya baiwa Amurkawa damar rike makamai, damar da ya ce tana cikin wani hali.
Facebook Forum