Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kafafen Yada Labaran Karya Ne Makiyan Amurkawa - Inji Trump


Shugaba Donald Trump

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kara iza wutar kalubalantar kafafen yada labarai a jiya juma’a, In da yayi amfani da kafar sadarwar zumuntar twitter da ya fi so. Inda ya rubuta a shafinsa cewa, “Kafafen yada labaran karya, sune makiyan al’ummar Amurka!”

Rubutun farko ya saka sunayen Jaridar The New York Times da Gidan Talabijin na CNN da kuma Kafar yada labarai ta NBC a cikin jerin sunayen da ya lissafo. Rubutun ba dade da mannawa ba a ka goge shi, daga baya kuma ya maye gurbin sa da wani makamancin rubutun da ya kara da sunayen kafafen yada labaran cikin gida guda biyu wato ABC da kuma CBS.

Wannan sukar a shafin abotar yanar gizon, na daya daga cikin jerin hanyoyin da Trump yake amfani da su wajen sukar kafafen yada labarai, kuma ya zo ne bayan Shugaban kasar ya bar birnin Washington domin ziyarar kamfanin kera Jiragen Sama na Boeing Aircraft da ke Jihar Carolina ta Kudu. Daga baya shugaban ya nufi katafaren gidansa da ke garin Mar-a-Lago a jihar Florida.

Inda zai yi hutun karshen mako. Amma kuma cece-kuce ya barke a kafafen yada labarai da kuma kafafen sada zumuntar intanet game da muhimmancin ikirarin Trump ga manya manyan gidajen jaridun na Amurka a matsayin makiyan Al'umma. Muryar Amurka ta tuntubi fadar White House domin neman Karin bayani akan rubutun na twitter amma babu amsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG