Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hankalin Trump Zai Koma Wasu Lamuran In Inshorar Lafiyarsa Ta Fadi A Majalisa


Majalisar Dokokin Amurka

Shugaban kasa Donald Trump yayi barazana ga ‘yan Jam’iyyarsa ta Republican da in suka bar Inshorar lafiya ta Obamacare ta ci gaba zai mayar da hankalinsa kan wasu al’amurran.

Shugaban ya sha alwashin cewa zai soke kuma ya maye gurbin tsarin inshorar wacce aka fi sani da Obamacare. Ba’a tabbatar da hakikanin abin da ya faru ba, bayan zaman sasantawa da kai komo da aka yi ta yi a cikin majalisar dokokin.

Kuma har zuwa yanzun nan ba tabbacin ko Yan Republican suna da ishashshen goyon baya da zai sa a amince da wannan shirin.

Trump ya baje kolin kwarewarsa ta shirya ciniki a kan gaba, amma ya kasa samun nasarar shawo kan ‘Yan ra’ayin rikau na majalisar kuma hatta wasu masu sassaucin ra’ayin na fargabar makomarsu a siyasance idan suka dauki matakin da ba shine mazabunsu ke so ba.

Rashin nasarar Trump da ta Kakakin Majalisa Paul Ryan kan samu ishashshiyar kuri’ar goyon baya da zai hada kan jam’iyyar Republican ya jawo tirka tirkar siyasar da zai yi wahala su iya kauce mata koda kuwa anyi nasarar amincewa da dokar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG