Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Yana So Rasha Ta Dawo Cikin Kungiyar G-7


Bayan da aka fitar da Rasha daga cikin kungiyar manyan kasashe masu karfin tattalin arziki ta G-7 a shekarar 2014, yanzu haka shugaba Trump ya na so ta dawo cikin kungiyar.

Jiya Laraba Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ya na so kasar Rasha ta dawo cikin kungiyar manyan kasashe 7 dinnan mafiya karfin tattalin arziki, ko G-7 a takaice, duk da ci gaba da rike yankin ruwan Crimea, mallakin kasar Ukraine, da Rashar ke yi.

An fitar da Rasha daga kungiyar ce saboda yin gaban kanta da ta yi wajen hade yankin ruwan a 2014.

Yayin da shugabannin kungiyar ta G-7 ke kama hanyar zuwa garin Biarritz na gabar tekun Atlantika a kasar Faransa, don yin taronsu na shekara-shekara a wannan satin, Trump ya ce zai yi ma’ana Shugaban Rasha Vladimir Putin ya dawo cikin wannan kungiyar.

Trump ya nuna alamar rashin damuwa da yadda kasar Rasha ke ci gaba da daukar Crimea a matsayin yankin kasarta, a maimakon haka ya na ganin laifin tsohon Shugaban Amurka Barack Obama, saboda hade yankin na Crimea da Rasha ta yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG