Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Mai Jiran-gado Trump Zai Kyale Takunkumin Da Amurka Ta Azawa Rasha.Amma.......


Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump.
Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump.

Trump ya fadawa wata jarida cewa idan Rsha ta bada hadin kai zai yi nazarin janye su.

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, yace zai ci gaba da aiki da takunkumin da gwamnatin shugaba Obama ta kakabawa Rasha, amma zai duba janye su,muddin Rasha ta bada hadinkai, tayi aiki da Amurka kan muradun da suke da muhimanci ga duka sassan.

Trump wanda ya bayyana haka a hira da jaridar Wall Stret, yace idan Rasha ta hada kai wajen yaki da ta'adanci da kuma akan wasu muhimman batutuwa, wa- zai bukaci takunkumi, idan muna shiri da Rasha, kuma tana ayyuka masu kyau?

Amurka ta azawa Rasha takunkumi na farko ne a shekara ta 2014 bayan da Rasha ta kama zirin Crimea. Ranar 29 ga watan jiya kuma, shugaba Obama ya kori jakdun Rasha 35,ya azawa kasar karin wasu takunkumin saboda yunkurin da Moscow tayi na yin shishshigi a zaben Amurka da aka yi cikin watan Nuwamba a bara.

Haka nan Shugaban na Amurka mai jiran gado ya gayawa jaridar cewa, manufofin Amurka da suka ayyana Taiwan a zaman wani bangare na kasar China tilas a sake shawarwari akai. Kalaman da suka sha banban da abunda hadimansa suka fada, lokacinda Trump yayi magana ta woyar tarho da shugabar Taiwan, bayan da ya sami nasara a zaben na Amurka.

A gefe daya kuma, Mr.Trump ya caccaki gwarzon yaki kare 'yancin tsiraru da bakar fatar Amurka dan majalisar wakilan Amurka John Lewis, wanda yace "Mr. Trump ba sahihin shugaban Amurka bane". John yace ya hakikance Rasha ta taimakawa Trump ya lashe zabe.

Trump ta shafinsa na Twitter yace, maimakon sukar sa da Lewis yake yi, ya maida hankali wajen bautawa wadanda suka tura shi majalisa.

XS
SM
MD
LG