Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Rufe Gwamnati Idan Majalisa Bata Bashi Kudin Gina Katanga Kan Iya Da Mexico Ba


Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka ya yi barazanar rufe gwamnati idan majalisa bata bashi kudin isasshen kudin gina katanga ba akan iyaka da kasar Mexico a kasafin kudin Satumba lamarin da masu kula da alamuran siyasa suka ce 'yan jam'iyyarsa ba zasu lamunta da yunkurin ba.

Shugaban Amurka Doanld Trump yayi barazanar zai daukar matakai da zasu kai ga rufe ko dakatar da aiyukan gwamnati a wani lokacin nan gaba a banan nan, idan majalisar dokokin Amurka bata amince da isassun kudi domin tsaro akan iyaka ba, ciki harda kudi domin gina katanga kan iyakar Amurka da Mexico.

A watan jiya ne dai shugaba Trump ya sanya hanu kan kasafin kudi dala triliyan daya da milyan dubu dari uku wadda za su yi aiki har zuwa watan Satumba karshen shekarar kudi a Amurka.

Da yake magana a wani gangamin yakin neman zabe a garin Washington a jahar Michigan, Mr. Trump yace, a ranar 28 ga watan na Satumba wakilan majalisa zasu kada kuri'a kan sabon kasafin kudi, kuma idan basu ware kaso domin aikin ginin katangar ba, ba zai sanya hanu akai ba.

Amma sai ta yiwu 'yan uwansa a siyasance na jam'iyyar Republican, ba za su goyi bayansa ba, idan yayi kokarin dakatar da aiyukan gwamnati gabannin zaben rabin wa'adi da za'a yi cikin watan Nuwamban na bana ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG