Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Sake Fito Da Dokar Hana 'Yan Wasu Kasashe Shiga Amurka


Donald Trump
Donald Trump

Duk da cewa Alkalai a Amurka sun takawa dokar farko birki, yanzu haka gwamnatin Trump na ci gaa da yiwa dokar kwaskwarima don sake gabatar da ita.

Shugaban Amurka Donald Trump zai ci gaba da kare dokar da ya fitar a wajajen karshen watan daya, wacce ta takaita balaguron 'yayan wasu kasashe bakwai zuwa Amurka, dokar da aka yiwa kwaskwarima, kuma aka jin gwamnati zata kammala aiki akan dokar cikin kwanaki masu zuwa, inji mataimakin shugaban Amurka Mike Pence.


Mataimakin shugaban kasa Pence wanda ya bayyan ahaka a shirin talabijin na CBS jiya Laraba, yace ba wai kadai shugaban zai ci gaba da kare matakin da ya dauka tun farko a gaban kotuna ba, sun hakikance cewa matakin d a shugaban na Amurka ya dauka yana karkashin ikonsa.


Kotunan Amurka sun takawa dokar birki, wacce ta hana 'yan kasashen Iraqi, da Iran, da Libya, da Somalia, da Sudan,da Syria da Yemen zuwa Amurka. Hakan nan dokar ta dakatar da shirin karbar 'yan gudun hijira zuwa Amurka.
Fiyeda kararraki daban daban har 27 aka shigar gabvan kotunan Amurka kan wannan batu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG