Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Shugaba Trump na Farko Gaban Majassar Tarayyar Amurka


Shugaba Donald Trump yayi jawabi karo na farko gaban majalissar tarayyar Amurka a daren jiya Talata.

A jawabinsa na farko gaban majalissar tarayyar Amurka, shugaba Donald Trump ya gabatar da jawabi mai armashi a yammacin jiya Talata fiye da jawabin da ya yi a ranar da aka rantsar da shi makwanni shida da suka shude.

Ya fada cewar lokaci karamin tunani da kananan fadace-fadace ya wuce.

Sai dai hankula sun karkata kan kalaman yaki da “’yan ta’addan Islama” da Trump ya ambata, kalaman da kafofin yada labarai suka nuna cewa mai bashi shawara kan harkar tsaro, Laftanar Janar H.R. McMaster da wasu mukarrabansa suka bashi shawarar ya daina fada.

McMaster ya fadawa ma’aikatansa a makon da ya gabata cewar ya fi ra’ayin amfani da Kalmar masu tsattsaurar ra’ayin Islama wurin kiran magoya bayan gwamnatocin kasashen Musulmi da al’ummar Musulmin a maimakon ganin kowane Musulmi a matsayin dan ta’adda.

A kan batun masu kiran kansu kungiyar Musulmi ta IS, Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da yin aiki da kawayenta, ciki har da na kasashen Musulmi don kawar da munanan rikicin da abokan gaba suka haddasa a duniya.

Mutane da dama ne suka kalli jawabin shugaban Amurka Donald Trump da yayi gaban majalisun kasar a wurare dabam dabam.

Wasu dai sun kalli jawabin ne a zauren taron majalisar wakilan kasar. Wasu kuma sun kalla ne a kan babban majigi dake bowling Aalley a Pennsylvania, hakazalika wasu sun kalla a gidan kallon dake Las Vegas.

An samu kuma ra’ayoyi dabam dabam a kan jawabin na shi. Wasu sun kyautata zaton cewa Amurka ta dauki hanyar gyaruwa wasu kuma na ganin tamkar shugaban ba shi da tsarin da zai cika alkawuran da ya dauka kuma ma bai san ta yadda zai cimma burinsa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG