Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Yanke Shawara A Makoni Biyu


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Watakila Shugaba Donald Trump ya sauya ra'ayin sa akan batun sauyin yanayi ko kuma ya tsaya kan bakansa

Shugaba Donald Trump yayi alkawari, cikin makoni biyu masu zuwa zai yanke babar shawara akan yarjejeniyar sauyin yanayi da aka kula a birnin Paris na kasar Faransa

Shugaban yayi wannan furucin ne jiya Asabar da maraice a wajen gangamin cika kwanaki dari da yayi akan ragamar mulki da aka yi a garin Harrisburg jihar Pennsylvania.

A lokacinda ya fara gabatar da jawabi sai da aka fitar da wani mai zanga zanga. Shugaban yace a fitar da mutumin.

Ya baiyana irin nasarorin da yace gwamnatin sa ta samu cikin kwanaki dari, ciki harda tabbbatar da nadi alkalin kotun koli. Ya kuma ce akwai kyakyawar dangantaka tsakanin Amirka da China da kuma Britanniya.

Shugaban ya sake nanata alkawarin da yayi lokacin yakin neman zabe na gia Katanga tsakanin Amirka da Mexico.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG