Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Zabi Babban Alkalin Kotun Kolin Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump.

Yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke shrin nada babban alkalin kotun kolin Amurka, har an fara karce kasa tsakanin 'yan ra'ayin rikau da 'yan gaba-dai gaba-dai

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi tankade da rairaya game da sunayen mutanen da zai zabi Babban Alkalin Kotun Kolin AMurka daga cikinsu, inda yanzu mutane biyar su ka rage kuma biyu daga cikinsu mata ne. Ya ce ranar 9 ga watan gobe zai bayyana wanda ya zaba.

Shugaba Trump zai gabatar da sunan mutumin da zai gaji Babban Alkalin Kotun Kolin Amurka Anthony Kennedy wanda ke shirin yin ritaya.

Shugaba Trump ya gaya ma manema labarai a cikin jirgin saman fadar Shugaban kasa na Air Force One jiya Jumma'a cewa mai yiwuwa ma ya fara tambayoyin tantance mutane biyar din a wannan karshen makon a Bedminster, New Jasey, inda zai dan huta da iyalinsa a gandun wasan kwallon golf dinsa.

Trump ya ce daga cikin tambayoyin da zai yi ma mutane biyar din babu batun sanin matsayinsu kan damar zubar da ciki, wanda Kotun koli ta yanke hukunci a kai a baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG