Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaida Jonathan Takara Shi ne Mafi A'ala Inji Bello Halliru


Bello Halliru PDP.
Bello Halliru PDP.

Bello Halliru ya fadi hakan ne a wata hira da Aliyu Mustaphan Sokoto.

A cewar tshohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan sadarwar Nageriya, bawa shugaba Goodluck Jonathan damar sake tsayawa takara shine abun da yafi chanchanta, saboda yin hakan zai kwantar mai da hankali, yakuma bashi damar ya meda hankali don tunkarar matsalolin kasar batare da wani tunani cewar wani na neman wannan kujerar tashi ba.

Tsohon shugaban jam’iyar ya kuma yi Karin haske kan cewar ita jam’iyar ta PDP zata goyi bayan duk wani dantakararta amma bazata tsaida dan takaraba da cewar babu wanda zaiyi jayayya da shi ba a kowane mataki.

Ya kuma yi nuni da cewar idan akwai masu jayayya da matakin da jam’iyyar ta dauka na tsayar da shi shugaban kasar, to za’a yi zaben cikin gida.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG