Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsare Dasuki Ba Bi-Ta-Da-Kulli Ba Ne - Malami


Ministan shari’a kuma Antoni janar din gwamnatin tarayyar Najeriya, Abubakar Malami ya musunta zargin cewa gwamnati tana yiwa tsohon mai bada shawara a kan tsaron kasa, Sambo Dasuki bita-da-kulli. Yace kotu ta tabbatar da zargi a kansa kuma ta yi masa shari’a kamar yanda take yiwa duk wani dan kasa.

Ministan shari’ar ya ce, maganar bita-da-kulli bata taso ba, saboda ana tuhumarsa da laifi mai karfi kuma wajibi ne a saurari bahasi daga gare shi. Ya kara da cewa inda babu zargin aikata laifi a kan Dasuki, ana iya cewa an yi masa bita-da kulli.

Antoni Janar ya yi wadannan kalaman ne a wata hira da ya yi da Muryar Amurka a kan sakin Sambo Dasuki tsohon mai bada shawara a kan tsaron kasa, wanda ya kwashe shekaru hudu yana tsare a hannun hukuma.

A ranar Talata ne hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta saki Dasuki tare da wani dan rajin kawo sauyi, Omoyele Sowore, biyo bayan wani umarni da ta samu daga gwamnatin tarayya. Ministan shari’ar da sanya hannu a kan umarnin sakin tsohon babban jami’in tsaron ya ce, shawarar sakin mutanen biyu ya biyo bayan beli da kotu ta basu.

Da yake amsa tambayoyi da Muryar Amurka ta yi masa a kan zargin da ake yiwa gwamnati na yin biris da laifukan wasu jami’an tsohuwar gwamnati amma ta kama Dasuki saboda ya taba kama shugaba Buhari a shekarun baya, Abubakar Malami ya ce, wannan gwamnati ta gurfanar da duk wanda aka same shi da aikata laifi a gaban kotu kafin a bashi beli.

A tattaunawar da Muryar Amurka ta yi da tsohon mai bada shawara ga tsaron kasar jim kadan bayan sakin shi, ya ce shida lauyoyin sa zasu yi nazari a kan matakin da zasu dauka nan gaba kana ya ce, yana cikin koshin lafiya.

Ga dai hirar da Ministan shari’ar Abubakar Malami da Muryar Amurka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG