Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaro: Matakan Da Muke Dauka Na Tasiri - Gwamnatin Zamfara


Lokacin da al'umar wani yankin jihar Zamfara ke zanga zanga saboda matsalar tsaro
Lokacin da al'umar wani yankin jihar Zamfara ke zanga zanga saboda matsalar tsaro

Sai dai gwamnatin adawa ta APC da ta gabata, ta bayyana damuwa ga wannan tsari na sulhu, wanda ta ce ta yi irinsa a can baya amma bai samu nasara ba.

Bayan kwashe tsawon shekaru kusan 10 ana tashe-tashen hankali, da hare-hare, da satar shanu da mutane domin karbar kudin fansa a jihar Zamfara, sabuwar gwamnatin jihar na ganin yanzu lokaci ne na zaunawa a teburin sasantawa, domin kawo karshen al'amarin, wanda ya lakume dubban rayuka a jihar.

Faruk Ahmed Gusau, wanda na daya daga cikin mambobin kwamitin da gwamnati ta kafa domin shawo kan lamarin, ya ce an fara daukar matakan da suka dace.

A matakin farko, a cewar shi, an soma samun nasarar karbo mutanen da dama da ‘yan bindigan jihar suke rike da su.

Wasu rahotanni na nuni da cewa sabon tsarin ya kunshi musayar fursunoni tsakanin ‘yan bindigar da gwamnati a karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan jihar, a wasu lokutan ma har da kudade.

Sai dai gwamnatin adawa ta APC da ta gabata, ta bayyana damuwa ga wannan tsari na sulhu, wanda ta ce ta yi irinsa a can baya amma bai sami nasara ba.

Amma wasu da dama a jihar na ganin, akwai banbanci tsakanin irin tsarin da wannan gwamnati ke bi da wacce ta gabata.

Yanzu haka dai wasu jama’ar jihar na bayyana cewa an samu raguwar kai hare-hare, da satar jama’a a jihar, duk da yake suna cike da fatan ganin ‘yan bindigar sun ajiye makamansu, a daidai lokacin da wasu ‘yan gudun hijira suke soma komawa gidajensu.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG