Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Taro A Abuja

Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja
Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja

Tsofaffin Sanatoci da ke karkashin inuwar Jamiyyar APC mai mulki a Najeriya sun yi gagarumin taron inda suka kafa kwamiti na musamman da zai yi tuntuba a gabanin zaben sabbin shugabanni a Majalisar dokokin kasar.

ABUJA, NIGERIA - Wannan shi ne karo na uku da tsofaffin Sanatoci daga Jumhuriya ta biyu zuwa Jumhuriya ta hudu a karkashin Sanata Bashir Lado za su yi wannan irin taron a babban birnin tarayya Abuja.

Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja
Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja

Shugabannin sun sha alwashin hada kan masu ruwa da tsaki don tabbatar da fitowar Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin a matsayin shugaban Majalisar Dattawa da mataimakin sa a Majalisa ta 10.

Shugaban tawagar Sanata Bashir Lado ya yi karin bayani cewa wannan taro ne na nuna wa 'yan uwa cewa ita Jamiyya ita ce uwa ita ce uba, kuma a dalilin Jam’iyya ce kowa ya kai inda ya kai a yau

Lado ya ce idan Jamiyya ta fito ta bada umurni, ya kamata kowa ya bi umurni, domin Jam’iyya ce ta haifar da shugabancin nan. Lado ya ce wadannan mutane da Jam’iyya ta zaba sun cancanta, kuma jam’iyya ta nuna adalci ne a kasa a yadda ta kasa mukaman saboda a samu zaman lafiya a kasar.

Daya cikin 'yayan Jamiyyar kuma wanda ya sauka daga neman mukamin shugaban Majalisar Dattawa saboda ya fito daga Jihar da mataimakin shugaban kasa ya fito, Sanata Mohammed Ali Ndume ya yarda cewa Jam’iyya ce kan gaba a harkar Majalisa kuma ya fi ganin sa a hanya da za ta tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja
Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja
Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja
Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja

Ndume ya ce dukan wadanda suka taru a lokacin wanna gagarumin taro duk masu girmama Jam’iyya ne, tunda Jam’iyya ta fito da tsari, kuma wannan tsari an yishi ne saboda adalci domin a ba kowane bangare dama saboda kar a cuci kowa.

Ndume ya ce wani abu da ya ke bata masa rai shi ne batun kudi da ya ke taka rawa a harkar shugabancin Majalisa. Ndume ya ce wannan yana bata masa rai sosai, amma kuma yana ganin cewa mu'amalar kudi ba zai yi tasiri ba.

Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja
Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja

To ko wane mataki taron ya dauka na ganin an samun nasarar tsayar da wadanda Jam’iyya ta tsayar?

Sanata Bashir Lado ya yi karin haske cewa an kafa komiti mai karfi wanda zai tuntubi sauran ‘yan takarar kujerar shugaban Majalisar Dattawan da na kakakin Majalisar wakilai saboda a ja hankalin su wajen bin umurnin Jam’iyya.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Tsofaffin Sanatoci Na Karkashin Jam’iyyar APC Sun Yi Wani Gagarumin Taro A Abuja.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG