Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsoffin ministocin Faransa mata zasu fasa kwai akan cin zarafin mata


Shugabar asusun bada lamuni ko IMF kuma tsohuwar ministar kudin Faransa

Mata sun dade suna korafin ana cin zarafinsu a harkokin suyasar kasar Faransa lamarin da wasu tsoffin ministoci mata suka ce yanzu kam sun daina rufe bakinsu, zasu fasa kwai.

Tsoffin ministocin kasar Faransa mata su bakwai da suka hada da shugabar asusun bada lamuni ta IMF Christine Lagarde sun lashi takobin tunkarar cin zarafin da ake yiwa mata a harkokin siyasar kasar ta Faransa.

Jiya Lahadi a cikin mujallar da ake bugawa mako mako a kasar, wato Jornal Du Dimanche, matan suka lashi takobin wallafa duk furucin cin zarafi da musgunawa mata da ake yi da kuma irin halayyar da maza 'yan siyasa ke nuna musu.

Barazanar daukan wannan matakin ya biyo bayan wasu mata guda tara da suka koka tare da zargin cewa mukaddashin kakakin Majalisar Wakilan Faransa ya ci zarafinsu.

Tuni dai mukaddashin kakakin Dennis Baupin ya yi murabus saboda lamarin kodayake ya musanta zargin da matan tara suka yi tare da yin alkawarin kalubalantar zargin.

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG