Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Firayi Ministan Malaysia Mai Shekaru 92 Ya Lashe Zaben


Mahathir Mohamad, tsohon Malaysian firayim ministan Malaysia mai shekaru 92 ya lashe zaben kasar da aka yi jiya Laraba
Mahathir Mohamad, tsohon Malaysian firayim ministan Malaysia mai shekaru 92 ya lashe zaben kasar da aka yi jiya Laraba

Mahathir Mohammad tsohon firayim ministan Malaysia kuma dan shekaru 92 ya yi abun tarihi a duk duniya ya lashe zaben kasarsa ya kuma kawar da jam'iyyar da ta yi shekaru 60 tana mulki tun daga lokacin da kasar ta samu 'yancin kai

Tsohon firayi ministan Malaysia Mahathir Mohamad mai shekaru 92 da haifuwa , ya ba duniya mamaki da ya lashe zaben da aka yi jiya Laraba na yan majalisa bayan ya yi ritaya.


Mahathir da hadakar jami’iyun adawa da ake kira Alliance of Hope, sun kayar da jami’iyar National Front Coalition, wacce take mulkin kasar tun lokacin da kasar ta samu yancin kai a shekarar 1957.


Ana sa ran jami’iyar Alliance of Hope zata lashe kujerun majalisa 115, yayin da National Front Coalition kuma zata samu kujeru 79.


Masana sun yi has ashen National Front mai mulki zata yi hasarar kuri’ar farin jinni, amma zata ci gaba da samun rinjayin majalisa, bayan ta sake tsara taswirar zaben kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG