Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Gwamman Adamawa Zai ‘Daukaka ‘Kara


ADAMAWA: Kotu ta daure Barrister Bala Nigilari, tsohon gwamnan Adamawa
ADAMAWA: Kotu ta daure Barrister Bala Nigilari, tsohon gwamnan Adamawa

Tsohon gwamnan jihar Adamawa da kotu ta daure na tsawon shekaru biyar a gidan kaso, Bala James Ngillari, tare da kwamishinoninsa da magoya bayansa sun ce zasu daukaka kara game da hukuncin.

Tuni dai wannan hukuncin kotun jihar Adamawan ya bude wani babi a yaki da cin hanci da rashawa da kuma sabawa ka’idojin aiki.

Shi dai tsohon gwamnan da yanzu haka ke gidan yari, Barista Bala James Ngillari, tare da magoya bayansa da suka hada da tsoffin kwamishinoni da hadimai da kuma sauran wadanda suka rike mukaman siyasa a zamaninsa tuni suka nufi kotun daukaka kara domin kalubalantar wannan hukunci da suke ganin akwai abin dubawa.

Da yake Karin haske tsohon kwamishinan yada labarai a zamanin Bala James Ngilarin, Abdullahi Adamu Prembe, ya ce suna da kwarin gwiwar samun nasara a kotun daukaka kara.

Wannan matsalar dai ta taso ne sakamakon kin bin ka’idar ayyukan hukumar kula da sayan kayakin gwamnati wato Bureau For Public Procurement BPP a takaice, lamarin da yasa aka kai ruwa rana har ta kai ga tunbuke babban daraktan hukumar

Tuni dai hukuncin kotun ya bude wani babi a yaki da cin hanci da rashawa da kuma sabawa ka’idojin aiki yayin da ya zuwa yanzu an zura ido aga yadda zata kaya a kotun daukaka ‘kara.

Domin karin bayani ga rahoton Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG