Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Obadia Mailafia Ya Mutu


Dr. Obadia Mailafia (Hoto: Facebook/AIT Online TV)
Dr. Obadia Mailafia (Hoto: Facebook/AIT Online TV)

Marigayin ya rike mukamin mataimakin gwamnan babban bankin na Najeriya a tsakanin 2005 zuwa 2007. Sannan ya taba aiki a bankin raya kasashen Afirka na AFDB.

Rahotanni daga Najeriya na cewa tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Dr. Obadia Mailafia ya mutu. Shekarunsa 64.

Kafafen yada labaran Najeriya da dama sun ruwaito cewa marigayin ya rasu ne a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a tsakar daren ranar Asabar.

Marigayin ya rike mukamin mataimakin babban bankin na Najeriya a tsakanin 2005 zuwa 2007. Sannan ya taba aiki a bankin raya kasashen Afirka na AFDB.

Bayan barin aikin gwamnati, Mailafia ya shiga harkokin siyasa, inda har ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC)

Ya kuma kasance mai yin fashin baki da rubuce-rubuce ga kafafen yada labarai kan al’amuran yau da kullum musamma a fannin tattalin arzikin Najeriya.

Ya yi karatun digirinsa a Jami’ar Ahmadu Bello Zari a (ABU,) inda ya kammala a shekarar 1978. Shi ne ya zo na daya a ajinsu a lokacin.

Marigayin ya kasance daya daga cikin masu fitowa su soki lamirin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan yadda take tafiyar da al’amuranta musamman kan abin da ya shafi harkar tsaro.

A bara, marigayin ya taba bayyana cewa wani gwamnan arewacin Najeriya ne kwamandan kungiyar Boko Haram, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce har hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyace shi ofishinta da ke Jos.

Sai dai a lokacin da yake amsa tambayoyi, Mailafia ya fadawa jami’an DSS cewa, ba shi da wata hujja ko shaida da za ta tabbatar da zargin da ya yi kamar yadda rahotanni suka nuna.

An haifi Mailafia a kauyen Randa da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna a arewa maso yanmacin Najeriya.

XS
SM
MD
LG