Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Gayyaci Obadiah Mailafia Zuwa Ofishinsu


Wan dan sanda a Najeriya yayin wata zanga-zanga da aka yi a jihar Legas a shekarar 2014.
Wan dan sanda a Najeriya yayin wata zanga-zanga da aka yi a jihar Legas a shekarar 2014.

Rahotanni a Najeriya sun ruwaito cewa rundunar 'yan sanda a Najeriya sun gayyaci tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, Obadiah Mailafia zuwa ofishinta.

Rundunar ta bukaci Mailafia da ya bayyana a ofishinta na birnin Abuja a ranar Litinin mai zuwa.

Wannan sammacin na zuwa ne a lokacin da hukumar farin kaya ta DSS take bincikensa kan wasu zarge-zarge.

A cikin makon da ya gabata ne DSS ta gayyaci Mailafia da ya bayanna a ofishinta na Jos bayan da ya furta wasu kalamai a yayin wata hira da wani gidan rediyo inda ya zargi wani gwamnan Arewacin Najeriya da zama babban jigon Boko Haram.

A cewar wasu kafofin yada labaran Najeriya, wasikar wacce 'yan sandan ta aikewa Mailafia mai dauke da sa hannun mataimakin kwamishina Umar Mamman Sanda ta bayyana cewa tana kara bincike ne kan zarge-zargen da ya yi.

Tuni dai hukumar da ke kula da kafofin watsa labarai a Najeriya ta NBC ta ci tarar gidan rediyo na Nigeria Info wacce ta gudanar da hirar tasa. NBC ta ce Nigeria Info ya bayar da damar a wallafa labaran da za su iya kawo tashin hankali.

A yayin hirar Mailafia ya bayyana cewa ya samu labarin ne daga wasu tsoffin mayakan Boko Haram, amma daga baya a lokacin da ya ke bayar da hakuri kan kalaman nasa ya ce "na san ya kamata in yi bincike kafin in yi magana saboda watakila an ba ni labarin boge."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG