Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Ya Bada Shawarar A Rage Albashin Masu Rike Da Mukaman Siyasa


Kingsley Moghalu, tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya CBN
Kingsley Moghalu, tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya CBN

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Kingsley Moghalu,  ya yi kiran da a rage albashi da alawus-alawus na masu rike da mukaman siyasa har da na ‘yan majalisar dokokin kasar da kashi 50 cikin 100.

ABUJA, NIGERIA - To saidai wannan kira bai yi wa wasu 'yan Majalisa dadi ba, amma wani tsohon dan Majalisar Wakilai kuma kwararre a fannin siyasa ya ce suna goyon bayan irin wannan kira.

Kingsley Moghalu ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake magana a daya daga cikin gidajen telebijin din da ke kawance da Muryar Amurka mai suna Channels TV. Moghalu ya ce matakan gudanar da mulkin kasar na karfafa almubazzaranci a tsakanin shugabanin siyasa da wadanda aka nada.

Moghalu ya ce idan ana so a ci nasara dole ne a magance shi tun daga Shugaban kasa har zuwa kasa kuma dole ne ta hada da Majalisar Dokoki. Amma ‘dan Majalisar Wakilai daga jIhar Jigawa, Abubakar Hassan Fulata, ya ce wannan ba daidai ba ne saboda kudin da ya ke karba Naira miliyan daya ne da dubu dari daya a duk wata. Fulata ya ce yana mamakin yadda wannan batun kudin 'yan Majalisa ya tsone wa mutane idanu. Fulata ya ce ba a kyauta wa 'yan Majalisa ba, saboda ayyukan da suke yi wa kasa ba kadan ba ne da za a ce kudin su ya yi yawa har ana neman a rage.

Amma tsohon dan Majalisar Wakilai daga jihar Sokoto, Aminu Shehu Shagari, ya ce lallai yana goyon bayan kira da Moghalu yayi inda ya ce in za a rage kudaden ‘yan siyasa a rage wa kowa, daga manyan alkalai, ministoci da ‘yan majalisa, duk a rage masu kudade tun daga albashi zuwa alawus-alawus. Aminu ya ce kudaden da ake samu na shiga a kasar ya ragu kwarai da gaske kuma ba a samu kamar da.

Akwai abinda ake kira “Over Head” wato kudaden da ake kashewa wajen sayen kayan alatu a gidajen yan majalisa. Aminu ya ce ya kamata duk a rage,saboda ya sa ana ganin kaman aikin Majalisa ya tashi daga yin dokoki, ya zama na yin kudi.

Shi kuwa kwararre a fannin siyasar kasa da kasa kuma Malami a Jami'ar Abuja Dr. Farouk Bibi Farouk ya ce wannan kira abin dubawa ne inda ya ce ai ‘yan majalisa su ne masu sa idanu a harkar gudanar da Gwamnati tun daga kudaden da ake kashewa zuwa yadda ake samo kudaden. Farouk ya ce ana barnar kudi sosai a harkar gudanar da Gwamnati a Najeriya sabanin yadde ake yi a wasu kasashe. Farouk ya ce ‘yan Majalisa su ji tsoron Allah su duba yadda tsarin ya ke, su kyautata wa al'umma.

To saidai shugaban hukumar da ke kayyade kudaden manyan ma'aikatan gwamnati da na 'yan siyasa har da ‘yan Majalisu, Mohammed Bello Shehu ya ce an dade ba a kara wa 'yan siyasa kudi ba. Shehu ya ce tun shekara 2008 ne rabon da a yi wa manyan ‘yan siyasa karin kudi a wannan kasar, saboda haka ba abu ne da zai sa mutane su tada hankalin su ba. Shehu ya ce abu ne da yanayin kasa bai bari an duba yiwuwar kara kudaden ba.

Abin jira a gani shi ne irin martanin da mahukunta za su mayar kan wannan kira da tsohon mataimakin gwamnan CBN, Kingsley Moghalu, ya yi ko a yi wa yan siyasa da manyan ma'aikatan gwamnati ragin kudi ko a kara masu.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Ya Bukaci A Rage Albashin Masu Rike Da Mukamin Siyasa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG