Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Mataimakin Shugaban Sudan Ta Kudu Daya Ya Arce Na Kasar Congo


Tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu na ‘daya, Riek Machar, ya gudu ne zuwa makwabciyar kasarsa, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda ake tunanin ma bashi da lafiya.

A jiya Alhamis ne mai magana da yawun majalisar dinkin duniya, Farhan Haq, ke fadawa manema labarai cewa Machar da wata karamar tawagarsa suna Congo. An dai sanar da tawagar majalisar dinkin duniya mai aiki a can, wadda ake kira MONUSCO, cewa ya shiga kasar kuma an sanarwa da gwamnatin kasar. Gwamnatin kasar ta nemi ma’aikatan MONUSCO din da su ‘dauke su daga wani wurin da ke daura da kan iyakar DRC da Sudan Ta Kudu zuwa wani wuri a cikin kasar ta Congo, wanda mjalisar dinkin duniya ta ki bayyanawa.

Haq yace tawagar majalisar dinkin duniya da ke aiki a Sudan ta Kudu, babu hannunta a zuwan Machar Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.

Lokacin da aka tambayeshi ko Machar na bukatar kulawa ta lafiya, Haq ya ce “muna bashi duk kulawar da yake bukata.” Wasu kafofi sun fadawa Muryar Amurka cewa tsohon mataimakin na Sudan ta Kudu, bashi da lafiya ko ya samu rauni alokacin da sojojin kiyaye zaman lafiya suka gana da shi a Kongo.

Machar dai ya shiga buya tun farkon watan Yuli, biyo bayan arangama tsakanin magoya bayansa da sojojin gwamnati a birnin Juba, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300.

Shugaban kasa Salva Kiir ne ya kori Machar daga mukaminsa na mataimakin shugaban kasa na ‘daya, ya kuma maye gurbinsa da Taban Deng Gai.

XS
SM
MD
LG