Kwamitin sojan da ke Mulki a kasar da ake kira NCSP a takaice ya tsare Keita a lokacin da aka yi juyin mulki a kasar a makon da ya gabata, inda Keita ya sanar da cewa ya yi murabus jim kadan bayan aukuwar lamarin.
A lokacin da ya ke tsare, an bada rahoton cewa Keita ya ce ba tilasta ma shi aka yi ya sauka daga kan karagar mulki ba, kuma ba ya so ya koma, amma ya na so a koma wa tsarin dimokradiyya cikin sauri.
Majalisar Dinkin Duniya, tare da kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWA, ne suka bukaci a saki Keita, wanda kuma ake kira IBK a takaice.
Facebook Forum