Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Amurka G.H.W.Bush da Matarsa Suna Kwance Asibiti


Tsohon Shugaban Amurka George H. W. Bush mai shekaru 92 a duniya
Tsohon Shugaban Amurka George H. W. Bush mai shekaru 92 a duniya

Rahottani daga jihar Texas ta nan Amurka sun ce an kwatarda tsohon shugaban Amurka George Hebert Walker Bush da matarsa Barbara a assibiti.

Mr.Bush yana kwance ne a sashen kula da masu matsanacin ciyo na asibitin birnin Houston sakamakon kokarin da ake yi na ganin bude mishi hanyoyin shaker iska na makogaronsa.

Mai Magana da yawun iyalan gidan tsohon shugaban kasar Jim McGrath yace tsohon shugaban kasar yana murmurewa, amma dai zaici gaba da zama a wannan asibitin domin a cigaba da kula dashi.

Haka kuma McGrath yace ita ma matar tsohon shugaban kasar, watauBarbara Bush tana kwance a asbiti daya da mijin natadomin riga kafi ko tana fama da gajiya da kuma tari.

Bush, wanda shine Shugaban na Amurka na 41 a jerin shugabanni Amurka, an kaishi asibiti ne a ranar Asabar bayan da aka fahimci yana fama da matsalar nunfashi.

McGrath yace Bush mai shekaru 92 da haihuwa yana fama da matsalar ciwon huhu da kuma nimoniya.

Sailin da yake taron manema labarai na karshe a matsayin sa na shugaban Kasa, Shugaba Barrack Obama yace fadarsa ta White House tana tattaunawa da iyalan tsohon shugaban kasa Bush kan halin da yake ciki.

Obama yace Bush da matarsa Barbara ba wai sun sadaukar da rayuwarsu bane kurun ga Amurka a’a har kullun suna a zaman mutane ne dake bashi shawarwari nagari.

XS
SM
MD
LG