Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar Tandja Mamadou Ya Rasu


Tsohon shugaban Nijar Tandja Mamadou.
Tsohon shugaban Nijar Tandja Mamadou.

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa tsohon shugaban kasar Tandja Mamadou ya rasu bayan da ya yi fama da rashin lafiya.

Tanja ya rasu ne da yammacin Talata a Niamey babban birnin kasar.

Wata sanarwar daga fadar shugaban kasar Nijar ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar.

Sanarwar ta ce za a yi zaman makoki na kwana uku a duk fadin kasar.

Tarihin Rayuwar Tandja

An haifi Tandja ne a 1938 a Maine Soroa a yankin Tafkin Chadi a kudu maso gabashin Nijar.

Ya yi aikin soja, inda har ya kai mukamin kanar. A 1974 ya kasannce ya na da hannu a juyin mulkin da aka yi wa shugaban kasar na wancan lokaci Hamani Diori.

Tandja ya taba zama jakadan Nijar a Najeriya na tsawon shekara biyu.

Ya kuma ta ba zama ministan cikin gida na Nijar a 1990. Bayan ya yi ritaya daga aikin soja, ya yi yunkuri har sau biyu na zama shugaban kasar a shekarun 1990 amma bai yi nasara ba. Ya ci gaba da yin adawa da gwamnati inda har aka taba kama shi, kafin daga baya ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasar.

Rayuwarsa a Siyasa

Tandja ya zama shugaban kasar Nijar ne bayan ya lashe zaben 1999, inda ya sha alwashin dawowar zaman lafiya na siyasa a zaman wata hanyar sake gina tattalin arzikin kasar. An kuma sake zaben shi a karo na biyu a 2004.

A 2005, babbar jam’iyyar adawa a kasar ta yi wa Tandja kakkausar suka kan yadda ya tafiyar da matsalar yunwa lokacin da kasar ta yi fama da fari da kuma annobar fari wadanda suka lalata amfanin gona.

A 2009 lokacin da wa’adi na biyu na gwamnatinsa ya kare, Tandja ya shirya zaben raba gaddama na neman kara wani wa’adin mulki, yana mai cewa ‘yan kasar suna son ya ci gaba da mulki don tafiyar da aikace-aikacen samar da sinadarin uranium da kuma man fetur da kasar ta gano.

XS
SM
MD
LG