Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Kasar Brazil Ya Bada Kai Bori Ya Hau


BRAZIL - Brazilian President Luiz Inacio Lula da Silva during an act in Rio de Janeiro, Brazil, 02 April 2018 (issued 05 April 2018)
BRAZIL - Brazilian President Luiz Inacio Lula da Silva during an act in Rio de Janeiro, Brazil, 02 April 2018 (issued 05 April 2018)

Tohon shugaban kasa Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya mika kansa ga 'yansandabayan da aka basu umurnin su kame duk inda suka ganshi

Tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula Da Silva, wanda aka yankewa hukuncin zaman gidan yari, daga karshe ya mika kansa ga ‘yan sanda a jiya asabar, kwana daya bayan, yashiga wasan buya da ‘yan sanda da aka basu umurnin kama shi.

Da Silva ya bar ginin kungiyar maaikatar karfe inda ya nemi mafaka, kuma wurin da yake kewaye da masu gadin sa, da farko ma dai magoya bayan sa sunyi kokarin hana shi fita daga wurin.

Amma dai daga bisaani ya fito kuma da kansa ya shiga motar ‘yan sanda wacce ta wuce dashi zuwa caji ofis din dake Sao Polo, daga nan kuma aka dauke shi zuwa birnin Curitiba inda can ne ofishin hukumar binciken yaki da masu cin hanci da rashawa take.

A jawabin sa na farko lokacin da aka bada sanarwan cewa a kama shi a ranar talata ya shaidawa taron magoya bayan sa a ranar jumaa cewa, kage kawai ake masa anayi masa bita da kulli ne kawai domin a hana shi tsayawa takaran shugaban kasa wanda za ayi a cikin watan oktoba.

Tun a ranar jumaa ne dai Da Silva yakamata ace ya fara zaman gidan yari na tsawon shekaru 12 akan laifin cin hanci da rashawa, amma maimako sai ya shiga wasan buya da jamiaan tsaro, domin ko ya tafi ofishin maaikatar karafa nakasar dake wajen birnin Sao Polo inda nan ne ya fara fice a matsayin shugaban kungiyar maaikata.

Sai dai duk da lauyan sa yayi kokarin daukaka kara a ranar Jumaa amma hakan bai cimma nasarar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG