Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Kasar Iraqi Jalal Talabani Ya Rasu a Kasar Jamus


 Jalal Talabani, tsohon shugaban Iraqi kuma jagoran kurdawa wanda Allah ya yiwa rasuwa jiya Talata a wani asibiti a birnin Berlin.
Jalal Talabani, tsohon shugaban Iraqi kuma jagoran kurdawa wanda Allah ya yiwa rasuwa jiya Talata a wani asibiti a birnin Berlin.

Tsohon shugaban kasar Iraqi kuma shugaban kurdawa ya rasu a Berlin , kasar Jamus yana da shekaru 83 da haihuwa a duniya

Tsohon shugaban Iraqi kuma jagoran Kurdawan kasar, Jalal Talabani, ya rasu a wani asibiti a Berlin, yana mai shekaru 83, kamar yadda jami’an Kurdawan suka bayyana.

Talabani, ya taba jagorantar daya daga cikin babban bangaren ‘yan adawa Kurdawa a Iraqi, kafin dakarun da Amurka ta jagoranta su kai mamayar da ta kifar da gwamnatin Saddam Hussein a shekarar 2003.

Ya kuma mulki kasar ta Iraqi daga shekarar 2005 zuwa 2014, inda ya taba sauka a mulki a shekarar 2012 domin zuwa neman maganin matsalar bugun zuciya da ya yi fama da ita.

Wani dan majalisar dokokin Iraqi kuma Bakurde mai suna Zana, ya kwatanta Talabani a matsayin shugaba daya tilo da rasuwarsa ta girgiza Larabawa da Kurda da sauran kabilun kasar.

A lokacin yana raye, Talabani, ya kwashe rayuwarsa ta siyasa yana kokarin dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin bangarorin da ke Iraqi tare da gwagwarmayar neman yancin gashin kan Kurdawa.

Shine kuma shugaban Iraqi kadai da ba balarabe, wanda aka mai kallon mutumin da ya assasasa hadin kai tsakanin al’umomin Iraqi.

Rasuwar tasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da hukumomin yankin Kurdawa a kasar ta Iraqi, suka gudanar da zaben raba gardama kan ballewa daga kasar ta Iraqi wacce ta kalubalanci zaben.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG