Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon shugaban kasar Zambia Frederick Chiluba ya mutu


Tsohon shugaban kasar Zambia, Frederick Chiluba.
Tsohon shugaban kasar Zambia, Frederick Chiluba.

Yau asabar tsohon shugaban Zambia Frederick Chiluba ya mutu. Ya mutu yana da shekaru sittin da takwas a duniya.

Wani mai Magana da yawun gwamnatin Zambia, yace a yau asabar tsohon shugaban kasar Frederick Chiluba ya mutu a gidansa. Mr. Chiluba ya mutu yana da shekaru sitttin da takwas a duniya. Mai Magana da yaweun gwamnati yace tsohon shugaban yayi fama da ciwon zuciya da kuma ciwon koda kafin ya mutu.

Mr Chiluba yaja ragamar mulkin Zambia daga alif dari tara da casa’in da daya zuwa shekara ta dubu biyu da biyu. Shine shugaban Zambia na farko da aka zaba bisa tafarkin mulkin democradiya.

Mr Chiluba ya dare kan ragamar mulkin ne bayan kasar tayi kusan shekaru talatin karkashin mulkin jam’;iyar guda daya, karkashin tsohon shugaba Kenneth Kaunda. Wata kotu birnin London ta samu tsohon shugaban da laifin sace miliyoyin daloli na kudin kasar. Wata kotu a kasar Zambia kuma ta wanke shi daga zarge zargen cin hanci da suka kunno kai daga zarge zargen cewa ya sace dala dubu dari biyar a lokacinda yake jan ragamar mulkin kasar.

XS
SM
MD
LG