Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Sojan Amurka Ya Hallaka 'Yan sanda Uku Da Raunata Wasu


An bayyana wani tsohon sojan Amurka a matsayin 'dan bindigar nan da ya bude wuta ya hallaka 'yan sanda uku, ya kuma raunata wasu uku da safiyar jiya Lahadi a birnin Baton Rouge dake jihar Louisiana.

Jami'an soja sun ce Gavin Long mai shekaru 29 da haihuwa 'dan birnin Kansas ta jihar Missouri, shi ne ya yi shigar bakaken kaya ya budewa 'yan sandan wuta. Ya yi aiki da sojojin ruwa tsakanin shekara ta 2005 zuwa 2010, har ya kai matsayin Sergeant. An kuma tura shi kasar Iraqi daga shekara ta 2008 zuwa 2009. An kashe shi a musayar wuta da 'yan sanda a jiya Lahadi.

Haka kuma ‘dan sanda na hudu da aka raunata, wanda mataimakin shugaban ‘yan sanda ne, na cikin mawuyacin hali a wani karamin asibiti inda akayi masa aikin tiyata.

Ana kuma duba wasu ‘yan sanda biyu a asibiti, amma basu ji mummunan raunuka ba.

Jami’an dai basu bayar da wata shaida da take nuna ‘yan sanda aka yi niyyar aunawa a wannan harin ba, daga baya dai shugaban ‘yan sandan jihar Col Mike Edmonson, ya bayyanawa manema labarai cewa masu bincike sunyi imanin cewa mutun shi kadai ne ya kai harin.

Amma kuma Edmond yayi gargadi kan cewa har yanzu ana nan ana gudanar da bincike. Kuma jami’ai basu kau da tunannin zai iya yiwuwa maharin ya samu taimakon wasu mutane ba.

A yayin da shugaba Obama ke magana ta gidan talabijin na kasa, ya yi Allah wadai da harin, inda yace irin wannan hare haren na ‘kara yawa. Ya kuma yi kira ga Amurkawa da su guji irin wannan akida.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG