Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tukur S. Tukur Dan Dugaji Ya Taka Rawa Sosai A Shiga Ta Harkar Wasan Kwaikwayo


Abubakar Dan Auta

A cikin hirarsa da filin "A Bari Ya Huce..." Abubakar Dan Auta ya kuma bayyana dangantakarsa da Nafisa Abdullahi - Wai shin 'yar'uwarsa ce da gaske?

Matashi, kuma mai tashe a harkar fina-finan Hausa na zamani, Abubakar Sulaiman, wanda aka fi sani da sunan "Dan Auta" ya tattauna da filin "A Bari Ya Huce..." na VOA Hausa, inda ya musanta rade-radin da wasu ke bazawa cewa ya rasu.

Dan Auta yace yana nan da ransa, kuma yana ci gaba da harkarsa ta yin fina-finai masu bayar da dariya, tare da gudanar da wasannin ban dariya a bainar jama'a. Haka kuma, ya bayyana gaskiyar dangantakarsa da wata 'yar wasan fim din Hausa da ake kira Nafisa Abdullahi, wadda akasarin mutane suka bayyana cewa 'yar'uwarsa ce.

A cikin wannan hirar da za a fara watsawa daga asabar 19 Maris 2011, Dan Auta yayi magana kan rawar da Tukur S. Tukur, wanda aka fi sani da suna Dan Dugaji, ya taka wajen shigar shi Dan Auta harkar fina-finai.

Ana iya sauraron wani bangaren wannan tattaunawa a kasa, ko kuma a can sama a gefen dama. A kasdance da filin "A Bari Ya Huce..."

Somin-Tabin Hira...

...Da Abubakar Sulaiman Dan Auta

XS
SM
MD
LG