Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tunbudin Tanderu: Ana Cikin Fargaba a Hawaii


Tunbudin tanderun narkakkun duwatsu a Kilauea na jahar Hawaii

Yayin da tunbudin tanderu ke karuwa a tsibirin 'Big Island' na jahar Hawaii ke ta karuwa, mazauna wannan tsibirin na dada nuna damuwa, a yayin da hukumomi kuma ke shirin fuskantar abin da ka faru.

Mazauna tsibirin Big Island da ke jahar Hawaii ta Amurka, na cigaba da zama cikin shirin ko ta kwana, bayan da tunbudin narkakkun duwatsu da ke malalowa daga Kilauea ya kwararo har zuwa sashin gabas na tsibirin, al’amarin da ya tilasta sake kwashe mutune.

Kamfanin Dillancin Labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa gidaje akalla biyar sun lalace, sanadiyyar cillowa daga karkashin kasa da tanderun ke yi suna fadawa kan gidaje.

Hukumar Nazarin Tanderu ta jahar Hawaii ta yi gargadi jiya Asabar cewa, “Hayakin da ke fitowa daga gidajen da ke cin wuta da kuma tanderun da ke konewa na da hadarin gaske ga lafiyar jama’a, saboda haka a kauce masu.”

Babu dai rahoton mutuwa ko jin rauni sanadiyyar wannan al’amarin. To amma ko ranar Jumma’a sai da jami’ai su ka yi gargadi cewa akwai sinadarin sulfur da yawa cikin iska wanda hakan ka iya hadari ga dattawa da kuma mutanen da ke da lalurar numfashi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG